Alhaji Ibrahim Abdullahi Tafashiya(SOLO) shi ne Madawakin Kankiya ya rasa rayuwarsa a jiya Asabar 22 ga Yuli 2023 a garin Kankiya sakamakon kisan gillar da wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne suka yi masa. Mummunan al'amarin ya faru ne da misalin karfe 08:30 na dare a unguwar low cost da ke bisa hanyar Kano a cikin garin na Kankiya, shi dai mamacin wanda ya kai ziyarar sada zumunci gidan kanen mahaifinsa Alhaji Garba Baraya wanda a lokacin baya gari, shedun gani da Ido sun ce bayan fitowarsa daga gidan ne ya lura da wasu mutane da bai gane ma wa ba, da suka zo suka raba shi suka wuce, kasancewar sa daya daga cikin 'yan kwamitin tsaro na garin Kankiya ya sa ya kasa hakuri, inda nan take ya yi masu magana da cewa, "bayin Allah kun zo kun wuce ba sallama"? Ba tare da sanin cewa miyagun suna dauke da muggan makamai ba, ya ce masu ku zo mu gaisa mana, inda su kuma ba su yi wata-wata ba nan take suka fito da bindiga su ka bude wuta. Mam...
SHAWARAR DA MAE GIRMA SARKI YA TATTAUNA DA SHUGABAN HUKUMAR KULA DA TSAFTACE MUHALLI ALH KABIR USMAN {AMOGA}.
Mai Martaba Sarkin Katsina ya shawarci Shugaban hukumar kula da tsaftace muhalli Alh. Kabir Usman (Amoga) da ya dauki mataki akan dukkan wanda ya karya doka. A ranar alhamis 20-07-2023 Sarkin yayi wannan yayin da tawagar hukumar karkashin jagorancin shugaban hukumar suka ziyarci fadar ta mai martaba Sarkin Katsina dake kofar soro nan cikin birnin katsina. Tunda farko dayake gabatar da jawabinsa shugaban hukumar ta tsabtace muhalli Alh Kabir Usman Amoga ya bayyana godiyarsa ga Allah tare da godiya ga mai martaba Sarkin Katsina akan wannan dama aka bashi Yaci gaba da cewa" mai girma Sarki nazo nan ne domin godiya da neman albarka a wajenka domin wannan mukami da na samu Allah ya bani ku kuka bani domin mai girma gwamna Mal Dikko Umar Radda dan wannan gida ne. Daga muna godiya gareka matuka kuma insha Allah zamuyi duk abinda ya kamata domin kawo ma wannan hukuma cigaba da ma jihar Katsina baki daya. Shima dayake gabatar da nasa jawabin mai ma...