SHAWARAR DA MAE GIRMA SARKI YA TATTAUNA DA SHUGABAN HUKUMAR KULA DA TSAFTACE MUHALLI ALH KABIR USMAN {AMOGA}.
Mai Martaba Sarkin Katsina ya shawarci Shugaban hukumar kula da tsaftace muhalli Alh. Kabir Usman (Amoga) da ya dauki mataki akan dukkan wanda ya karya doka.
A ranar alhamis 20-07-2023 Sarkin yayi wannan yayin da tawagar hukumar karkashin jagorancin shugaban hukumar suka ziyarci fadar ta mai martaba Sarkin Katsina dake kofar soro nan cikin birnin katsina.
Tunda farko dayake gabatar da jawabinsa shugaban hukumar ta tsabtace muhalli Alh Kabir Usman Amoga ya bayyana godiyarsa ga Allah tare da godiya ga mai martaba Sarkin Katsina akan wannan dama aka bashi
Yaci gaba da cewa" mai girma Sarki nazo nan ne domin godiya da neman albarka a wajenka domin wannan mukami da na samu Allah ya bani ku kuka bani domin mai girma gwamna Mal Dikko Umar Radda dan wannan gida ne.
Daga muna godiya gareka matuka kuma insha Allah zamuyi duk abinda ya kamata domin kawo ma wannan hukuma cigaba da ma jihar Katsina baki daya.
Shima dayake gabatar da nasa jawabin mai martaba Sarkin Katsina Alh Abdulmuminu Kabir Usman ya yi sabon shugaban hukumar murna akan wannan mukami da Allah ya bashi.
Ya kuma bashi shawarwari akan gudanar da aiki cikin tsari da kamanta adalci tare da kokarin kamantawa ba tare da la'akari da jam'iyya ko jinsi ba domin kawo ma wannan hukuma cigaba.
Daga karshe Sarkin ya jawo hankalin sa akan daukar mataki akan duk wanda yayi ba dai dai da kuma daukar matakai na tsabtace muhalli domin kare al'umma da kamuwa da cututtuka da kuma ambaliyar ruwa.
Tawagar da ziyarci mai martaba Sarkin ta kunshi manyan daraktocin hukumar da sauran ma'aikatan hukumar.
Danna nan domin ajiye comment 👇👇👇
Comments
Post a Comment
Daure kayi mamu comments domin ji daga gareka