DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI:
1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangijinka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.
2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.
3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.
4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.
5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.
6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).
7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka.
Allah Ka sanya wannan post ya zama sadakatul Jariya A Gare Ni Da Kuma Iyaye Na Da Duk Wanda Ya Taimaka Wajen yada shi
Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don Rahamar nan taka wacce ta yalwaci dukkan halittunka Ya Hayyu Ya Qayyum
Ku ajiye mamu comments naku anan:👇👇👇
Comments
Post a Comment
Daure kayi mamu comments domin ji daga gareka