MU LEKA MASARAUTAR KATSINA {MULMAK} NA MIQA SAQON GAESUWA GA DAUKACIN AL'UMMAR KANKIA DA MASARAUTAR KANKIA SAKAMAKON YANDA BARAYI SUKA HALLAKA MADAWKIN KANKIYA.
Alhaji Ibrahim Abdullahi Tafashiya(SOLO) shi ne Madawakin Kankiya ya rasa rayuwarsa a jiya Asabar 22 ga Yuli 2023 a garin Kankiya sakamakon kisan gillar da wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne suka yi masa.
Mummunan al'amarin ya faru ne da misalin karfe 08:30 na dare a unguwar low cost da ke bisa hanyar Kano a cikin garin na Kankiya, shi dai mamacin wanda ya kai ziyarar sada zumunci gidan kanen mahaifinsa Alhaji Garba Baraya wanda a lokacin baya gari, shedun gani da Ido sun ce bayan fitowarsa daga gidan ne ya lura da wasu mutane da bai gane ma wa ba, da suka zo suka raba shi suka wuce, kasancewar sa daya daga cikin 'yan kwamitin tsaro na garin Kankiya ya sa ya kasa hakuri, inda nan take ya yi masu magana da cewa, "bayin Allah kun zo kun wuce ba sallama"?
Ba tare da sanin cewa miyagun suna dauke da muggan makamai ba, ya ce masu ku zo mu gaisa mana, inda su kuma ba su yi wata-wata ba nan take suka fito da bindiga su ka bude wuta.
Mamacin cikin zafin nama yayi kokarin komawa cikin motarsa domin ya dauko bindigarsa, amma Ina kamin yayi wani abu har sun cimma sa inda suka zazzaga masa harsasai masu yawa a jikinsa suka hallaka shi, suka yi awon gaba da wayarsa da kuma bindigarsa.
An ce ko bayan kashe shi a bisa hanyar su sun yi garkuwa da wasu mutane uku a wani gidan biredi, amma daga bisani mutum daya ya kubce masu ya dawo. Har zuwa hada wannan rohoto ba a samu wani bayani dangane da sauran mutane biyun da suka tafi dasu ba.
Dubban jama'a ne suka halarci jana'izarsa yau Lahadi a garin Kankiya wadanda suka hada da Sakataren Gwamnatin jihar katsina Arc. Ahmed Musa Dangiwa, da Danmajalisar Dokokin Jihar katsina mai wakiltar Karamar Hukumar kankiya Hon. Salisu Hamza Rimaye, da Shugaban karamar hukumar Kankiya Hon. Musa Maikudi Kankiya, da Tsohon Danmajalisar wakilai Rt. Hon. Abubakar Yahaya Kusada, da sauran jama'a da dama daga ciki da wajen Kankiya .
Kamin rasuwarsa Alhaji Ibrahim Abdullahi Baraya ya taba zama kansilan ruko na mazabar Tafashiya/Nasarawa haka kuma shi ne jami'in kula da alhazai na karamar hukumar Kankiya a hajjin shekara ta 2022.
Tuni dai aka yi jana'izar sa kamar yanda addini musulinci ya tanada. Ga wasu daga cikin wadanda suka samu zuwa janazarshi kamar dae yanda zaku gani a hoton qasa akwae mae girma Sakataren gwamnan jihar Katsina {Arch Dangiwa), da Hon Abubakar Yahaya Kusada
Muna addu'ah tare da patan Allah Ubangiji Ya jiqan shi, Allah Ubangiji Yayi mashi rahma Ya kyautata makwancin shi. Allah Ubangiji Ya Yasa aljannah ce makoma agareshi da dukkan musulmae baki daya. Allah Ubangiji Yaba iyalanshi, danginshi, da dukkan musulmae baki daya haqurin rashi.
Ga dukkan masu buqatar yin ta'aziyya da addu'ah agareshi, zasu iya comment a qasa.👇👇👇
Comments
Post a Comment
Daure kayi mamu comments domin ji daga gareka