MAE MARTABA SARKIN KATSINA ALH ABDULMUMINU KABIR USMAN YA BUDE ASIBITIN JUSTICE UMAR ABDULLAHI, CON CLINICS DAKE A CIKIN GARIN KATSINA
Maimartaba Sarkin Katsina ya ƙaddamar da sabuwar Asibiti a Katsina
Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya jagoranci ƙaddamar da sabuwar Asibiti mai suna Justice Umar Abdullahi, CON Clinic a cikin birnin Katsina.
An assasa Asibitin ne domin sauƙaƙama Talakawan yankunan Unguwa Alƙali da sauran Talakawan birnin Katsina, inda aka assasa ta a ƙarƙashin ƙungiyar Ahalin Alƙali Hambali (Hambali Family Union).
Asibitin mai suna Justice Umar Abdullahi, CON Clinic tin daga yanzu ta cigaba da fara karɓar marasa lafiya a cikin Katsina kamar yadda Katsina Post ta samu.
Da yake gabatar da jawabinsa a lokacin buɗe Asibitin, Maimartaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, ya bayyana jin daɗin sa fili a yayin ci-gaban da aka kawo mishi a Garin sa.
Ya jinjina ma waɗanda suka jajirce don ganin an assasa Asibitin gameda taimakawa rayuwar Talakawa masu ƙaramin ƙarfi.
Tunda farko, yayi addu'ar Allah ya ƙara haɓɓaka jihar Katsina da samuwar inganta tsaro a jihar baki ɗaya, tare da ba waɗanda suka assasa Asibitin har cikin kabarin su bayan mutuwarsu.
Danna comment section domin yiwa mae girma sarki addu'ah tare da patan alkhaery.👇👇👇
Comments
Post a Comment
Daure kayi mamu comments domin ji daga gareka